Hukumar kula da cutuka masu saurinyaduwa a Nijeriya NCDC ta sanar da karuwar mutane 37 da suka kamu da cutar zazzabinLassa a fadin Nijeriya. Babban jami’in hukumar ChikweIhekweazu ya kara da cewa, mutanen sunkamu da cutar ne daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Fabarairu. Ihekweazu ya ce, a gwajin da sukagudanar a kan mutane 947 daga jihohi 20 da ake kyautata zaton su na dauke dacutar sun tabbatar da cutar a jikin mutane 324. Jami’in ya kuna ce, tun bayan sake barkewarcutar a farkon shekarar nan ta 2019 akalla mutane 69 ta hallaka a jihohi 20 Nijeriya. A karshe Chikwe Ihekweazu ya cedaga ranar 8 ga watan Fabrairu mutane 57 ne suka mutu sakamakon kamuwa dacutar, amma kawo yanzu adadin ya karu zuwa 69, matakin da ke nuna cewa cutar naci-gaba da yaduwa a Nijeriya.