Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Afrika ta YammaWAEC, ta bada sanarwar sakamakon jarabawar da dalibai su ka rubuta a cikinwatan Janairun da ya gabata. Wannan ne dai karo na biyu da aka kara samun gagarumar rashinnasara tun daga lokacin da aka fito da tsarin jarabawar a shekara ta 2018. Yayin da ake bayyana sakamakon jarabar a Ofishin Hukumar na Kasada ke Lagos, shugaban hukumar Isaac Adenipekun, ya ce dalibai dubu 12 da 202 nesu ka yi rajista, amma dubu 11 da 892 ne su ka rubuta jarabawar. Adenipekun, ya ce mutane dubu 3 da 102 ne kadai su ka samusakamakon sama da darussa biyar, wadanda su ka hada da Turanci da lissafi. Ya kuma tunatar da cewa a shekarar da ta gabata, kashi 17 darabi cikin 100 ne kacal su ka samu nasarar darussa biyar ko sama da haka. Adenipekun, ya ce an rike sakamakon jarabawar dalibai sama da300, saboda akwai zargin magudi ko satar jarabawa da ake yi masu.