Shugabankasa Muhammadu Buhari, ya taya Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti murnar zamasabon Shugaban kungiyar gwamnoni ta Nijeriya. Buhariya nuna yakinin cewa kowa ya yi na’am wajen zaben Fayemi, cewa hakan ya nunatarin karfin gwiwa da takwarorin sa ke da shi a kan sa. ShugabaBuhari, ya bukaci sabon Shugaban gwamnonin ya dauki zaben sa a matsayin watadama ta samun kwarin gwiwar yin aiki tare da gwamnatin tarayya, da sauranbangarorin gwamnati. Buhariya jadadda cewa, manufar kungiyar gwamnonin ita ce, sanya al’amurran ‘yanNijeriya sama da komai, tare da kauce wa bambancin akida da siyasa da addini kokabilanci. ShugabanBuhari, ya kuma nuna shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa kungiyar gwamnonin wajenaiwatar da manufofin ta. Yayinda ya ke yi wa Fayemi Kayode fatan kammala shugabanci cikin nasara, shugabaBuhari ya yaba wa shugaban kungiyar mai barin gado Abdul’aziz Yari na jiharZamfara.
Travel Report
Sabon-Zubi: Buhari Ya Taya Kayoede Fayemi Murnar Zama Shugaban Gwamnonin Nijeriya
Tags