Hukumarzabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fara raba kayayyakin zabe a daukacin kanananhukumomi 44 da ke Jihar Kano. Mataimakindaraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Garba Lawal ya bayyana hakaa wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya a Kano. Lawalya ce ma’aikatan hukumar INEC sun fara tantance kayayyakin zabe musammantakardun kada kuri’a a kowace karamar hukuma tun a ranar Larabar da ta gabata. Ajihar Kaduna kuwa, Hukumar INEC ta ce ta kai kayayyaki zabe a dukkan kanananhukumomi 23 da ke jihar, domin zaben gwamna da na majalisar dokokin jihar. BabbanJami’in yada labarai da hulda da Jama’a na INEC a jihar Kaduna, Sani Abdulfatahya bayyana haka ga kamfanin dillanci labaran Nijeriya da ke Kaduna. Abdulfatahya ce an rigaya an ware kuma an tantance dukkan kayan aikin zaben na kanananhukumomin jihar 23, wadanda za a yi zabe da su a mazabu 255 da kuma rumfunanzabe 5,102 da ke fadin jihar.
Coffee Digest
Zaben Gwamnoni: INEC Ta Fara Raba Kayayyakin Zabe A Kano Da Kaduna
Tags