Siyasar Kano na ci gaba janhankali, sakamakon girman hamayyar dake tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyuda ke kokarin lashe kujerar gwamna. Zaben ya fi jan hankali ne tsakaninjam’iyya mai mulki ta APC a jihar da kuma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP. Tun kafin a fara tattara sakamakonkananan hukumomi wani bangare na siyasar ta Kano ya fara murnar nasarar lashezabe, wani abin da ake gani zai haifar da rudani a jihar. Kano da ke da yawan kanananhukumomi 44, Sakamakon wani yanki na birnin Kano ba shi ne zai tabbatar dawanda ya ci zaben gwamna ba, sai idan an kammala tattara dukkanin sakamakon nakananan hukumomi. Rahotanni sun ce ko wasu kanananhukumomi da ke cikin kwaryar birnin Kanon inda ake murna babu wadda ta bayyanacewa ta kammala tattara sakamakon zaben na gwamnoni har ace an kai ga bayyanasakamakon. Sun ce za a iya samun tsaikun samunsakamakon wasu kananan hukumomi saboda rashin hanya mai kyau musamman irin suDoguwa, da Tudun Wada, da Rogo, da Kiru, da kuma Tsanyawa. Akwai manyan kananan hukumomi masumazabu 14 zuwa 13 wasu 10, inda za a iya daukar lokaci kafin tattara sakamakonzaben na gwamna.
Trade Brief
Zaben Gwamna: Siyasar Kano Na Ci Gaba Da Jan Hankali
Tags