Alamuna nuna cewa, wasu kwamishinonin zabe na jiha da na kasa za su yi murabus dagamatsayin su, biyo bayan zargin barazana da tozarci da kuma barazanar da rayuwarsu ta fuskanta daga hukumomin tsaro a lokacin zaben Shugaban kasa da na majalisuntarayya. Kwamishinonindai sun yi zargin cewa, sun kasance masu duba ga Shugaban hukumar a kan tarin hadurranda rayuwar su ke ciki, sai dai shi kan sa ya na fuskantar matsi da yawanhare-hare daga manyan mutane. Wasujami’an zabe na jiha da na kasa sun kasance a cikin tsoron cewa, ana iya kaimasu mumunan hari a ranar 9 ga watan Maris, yayin da za a gudanar da zabengwamna da na majalisar jiha. Wasumajiyoyi sun ce an yi garkuwa da wasu jami’an zabe a lokacin zaben, yayin dajami’an tsaron da za su ba su kariya su ka yi batan-dabo a lokacin da su ketsananin bukatar su. Majiyoyin sun kuma zargi hukumomin tsaro, ciki har da rundunar soji da sauran hukumomi da jan hankalin jami’an zabe, yayin da su ke ikirarin ba su kariya, a lokaci guda kuma su ka rika rarraba kayayyakin zabe ga ‘yan siyasa ba bisa ka’ida ba.
Sports Brief
An Samu Matsala: Manyan Kwamishinonin Hukumar Zabe Na Shirin Yin Murabus
Tags