Shugabankasa Muhammadu Buhari, ya karbi rahoton kwamitin bada shawara a kan yadda za afara biyan sabon karin albashi da majalisa ta amince da shi. Kwamitindai, ya mika wa shugaba Buhari rahoton ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Idandai za a iya tunawa, a ranar 9 watan Janairu ne shugaba Buhari ya kafa kwamitina karkashin jagorancin masanin tattalin arziki Bismarck Rewane, bayan jaddadaaniyar sa ta kara ma fi karancin albashin ma’aikata. ShugabaBuhari, ya fara bayyana niyyar sa ta yin karin albashin ne a watan Disamba nashekara ta 2018, yayin gabatar da kasafin kudi a gaban ‘yan majalisun dokoki natarayya. Yace kwamitin zai ba gwamnati shawarwari a kan yadda za ta samu sukunin biyanmafi karancin albashin ba tare da an samu hauhawar farashin kayayyakin masarufida matsalar rage yawan ma’aikata ba.Sai dai ministankasafi da tsare-tsare Udo Udoma, ya ce gwamnatin tarayya za ta kara yawan kudinharaji a kan kayan masarufi domin samun kudaden da za ta iya biyan sabon karinalbashin.