Jakadankasar Ghana a Najeriya Rashid Bawa, ya jaddada bukatar da take akwai na karainganta dagantakar dake tsakanin kasar sa da Najeriya. Bawaya bayyana hakan ne a lokacin bukin cikar kasar Ghana shekara 62 da samun ‘yancin kai wanda ya gudana a Abuja. Yace dangantakar dake tsakanin kasashen 2 na da matukar muhimmanci kuma sunataimakawa wajen ci gabansu ta bangarori da dama. Bawaya kara da cewa rashin samun daidaito a tsakanin kasashe na taimakawa wajenhaifar da talauci, cin hanci da rashawa da kuma durkushewar kasashen. Yace dangantakar dake tsakanin kasashen Nejeriya da Ghana, ya kara ingantabangarori da dama da suka hada da kasuwanci, zuba jari a cikin shekaru 3 dasuka gabata. Sannanya yi alkawarin cewa kasashen za su ci gaba da inganta dangantakar daketsakaninsu na ‘yan uwantaka, tare da yabawa gwamnati da ‘yan Najeriya kan yaddasuka natsar da kuwunansu a zaben da ya gabata.
Rural Journal
Diflomasiyya: Kasashen Najeriya Da Ghana Za Su Kara Inganta Dangantakar Dake Tsakanin Su
Tags