Uwargidar Shugabankasa, Hajiya Aisha Buhari, ta ziyarci wadanda ginin Ita-Faji ya rufta masu abirnin Lagas a babbar asibitin jihar domin yi masu jaje. Uwargidar shugan kasarta mika jajen ta ga wadanda lamarin ya ritsa da su, wanda ya yi sanadiyarmutuwar akalla mutane 20, ciki harda yaran makaranta. Aisha, wacce ta daukilokaci wajen ziyartan bangaren mata da kananan yara a asibitin, ta yi addu’arAllah ya ba iyalan wadanda suka mutu juriya da hakuri. Ta kuma yiwa wadanda kekwance a asibiti addu’ar samun lafiya. Daya daga cikin wadandaabun ya rutsa dasu kuma malama a makarantar benen da ya rufto, Easter Samuel,ta nuna alhini kan lamarin. Malamar mai shekara 19,wacce ke samun kulawa a asibitin tayi addu’ar Allah ya kare ta daga sakefuskantar wannan lamari a rayuwar ta. Shugaban likitocinasibitin, Gani Kale, ya ce yara 10 aka kwantar a asibitin bayan faruwarlamarin. Aisha ta samu rakiyan tsohon jigon Lagas a mulkin soji, ritaya Birgediya Janar Buba Marwa da tsohon mataimakin gwamnan jihar Plateau, Pauline Tallen da sauransu.