Hukumarhana yaduwar cututtuka ta kasa “NCDC” ta bayyana cewa, an samu karuwar yawanmutanen da suka rasa rayukan su sakamakon kamuwa da cutar zazzabin lassa a Nijeriya. Hukumarta ce karuwar masu fama da cutar da kuma wadanda suka mutu ya faru ne atsakanin watannin Janairu zuwa Maris. Bincikeya nyna cewa, hukumar ta yi wa mutane miliyan 3 da dubu 1 da dari 374 gwajincutar, sai dai mutane 420 daga cikin su sun kamu da cutar, sannan mutane 93 sunrasu a dalilin kamuwa da cutar. Ansamu barkewar cutar ne a kananan hukumomi 66 da ke jihohi 21 da suka hada daEdo da Ondo da Bauchi da Nasarawa, Ebonyi da Plateau da Taraba da Abuja daAdamawa da Gombe. Sauransun hada da Kaduna da Kwara da Benue da Rivers, Kogi da Enugu da Imo da Deltada Oyo da Kebbi da Cross River. Bincikeya nuna cewa an samu karin mutane 39 da suka kamu da cutar a wasu jihohi 6, saidai ba a samu wani ma’aikacin kiwon lafiya da ya kamu da cutar ba. Idanba a manta ba, tun da cutar ta bullo a wannan shekarar ma’aikatan kiwon lafiya15 ne suka kamu da cutar.
Rivers Report
Zazzabin Lassa: Kimanin Mutane 93 Suka Mutu A Najeriya
Tags