Rundunarsoji ta ce ta gano yadda wasu masu madafun iko a jihar benue ke haddasa rikicida daukar nauyin hare-haren da ake kai wa al’ummomin jihar. Tace hakan bai zo da mamaki ba, duba da irin harin da aka kai garin Agatu anamako daya kafin zaben shugaban kasa, da kuma harin Yammacin garin Gwer. Rundunarta ce ta fadada ayyukan ta a kan titin Loko zuwa Agatu, da Kwande da kumaiyakar garuruwan Benue, domin dakile hare-hare a nan gaba. Kwamandarrundunar Atisayen ‘Whirl Stroke’ Manjo Janar Adeyemi Yekini ya bayyana haka, acikin wata sanarwa da ya karanta yayin wani taron manema labarai a Makurdi. Yace ire-iren wadannan masu madafun ikon, su ke kara rura wutar rikici agaruruwan kamar yadda aka gani a lokutan baya, a kan irin hare-haren da akekaiwa jihar gabanin zaben shugaban kasa.