Sanatoci 64 da kuma‘yan majalisar wakilai su 151 ne ba za su dawo majalisar kasa a karo na 9 cikinwatan Yunin wannan shekarar ba. Sanatoci 45 da ‘yanmajalisar wakilai kimain su 209 kacal suka iya tsallake siradin zabukan da akagudanar a ranar Asabar idan aka yi la’akari da sakamakon zaben da Hulkumar INECta fitar. Sababbin da aka zaba su15 tsofaffin gwamnoni ne a jihohin su, 42 kuma daga cikin sanatoci 64 nasanatocin da basu dawo kan madafun ikon su ba sun gaza cin zabe a cikin watanOkotobar shekarar da ta gabata a lokacin zaben fid da gwani na jam’iyyun su. Sauran 22 sun sha kayene a zabukan da aka gudanar a ranar Asabar. Jam’iyyar APC mai mulkitana da sanatoci 64 da aka zaba a lokacin zaben na ranar Asabar, inda PDP takeda 41 sai kuma jam’iyyar YPP tana da sanata daya.
Innovation Report
Zaben 2019: Sanatoci 64 Da ‘Yan Majalisar Wakilai 151 Sun Dawo Gida
Tags