Shugaban kungiyar sayarda kayan miya wanda yake kula da kasuwancin bangaren tattasai a babbar kasuwarsayar da kayan gwari wadda take cikin unguwar Mile 12 a jihar Legas DaudaSuleman Tarai, ya bayyana cewa noman kayan miya da manoman Arewa ke yi yanataimaka wa Najeriya da al’ummar cikin ta baki daya. Dauda Sulaiman, ya yiwannan bayani ne a offishin sa da ke Mile 12 a lokacin da yake zantawa da wasumanyam manoman kayan miya daga Arewacin Nijeriya da suke kawowa Legas dominsayar wa al’umma. Ya kara da cewa yakamata gwamnatin tarayya da na sauran jihonin Arewacin Nijeriya a kokarin su nataima kama noman rani da na damina su kara kaimi a wajen bayar da tallafinnoman kamar yan da suka sabayi a kowace shekara domin kara wa manoman kwaringwiwa a wajen noman rani da na damina. Ya ci gaba da yin kiragwamnatocin da su ci gaba da ba manoman tallafin takin zamani da kayan feshi nakwari da sauran kayaiyakin da manoman ke am fani da su a wajen noman ranin da nadaminaSannan ya shawarcigwamnatocin da su bude kamfanonin da za a rika safarta kayan noman zuwagwangwani domin manoman su rage asarar rubewar tattasai da tumatiri kamar yaddawadan su kasashen da suka ci gaba suke yi a kasashen su