Direban jirgin saman daya dauko dan wasan kwallon kafar nan Emiliano Sala, bai kammala karatun sa amakarantar horar da matukan jirgin sama ba. Bincike ya nuna cewa DavidIbbotson, wanda shine ya tuka jirgin da ya yi hatsarin bai da cikakken lasisindaukar fasinjoji wanda hakan ya jawo ake tantamar watakila ba a bi tsarin dokaba kafin jirgin ya tashi. Har yanzu dai ba a ganogawar David, ba tun bayan da aka gano gawar dan wasan gaba na Cardiff CityEmiliano Sala, a ranar 6 ga watan Fabrairu. Wani rahoto da hukumardake bincike a kan hatsarin jirgin sama ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewaMista Ibbotson mai shekaru 59 yana da lasisin tukin jirgi a Burtaniya da Amurkawanda hakan na nufin ba zai iya daukar fasinjoji ba tsakankanin kasashenKungiyar Tarayyar Turai. Rahoton ya kuma bayyanacewa dole ne a gudanar da bincike domin sanin asalin Mista Ibbotson, da kumatarihin aikin da ya gudanar a matsayin sa na matukin jirgin sama. Jirgin saman dai ya yibatar dabo ne a ranar 21 ga watan Junairu dauke da dan wasan kwallon kafarwanda ya kammala shirye-shiryen komawar sa sabon kulob dinsa watau Cardiff dagaNantes.