MatarShugaban Kungiyar ‘yan jarida na Jihar Nasarawa Suleiman Abubakar ta samukubuta tare da sauran mata uku da aka yi garkuwa da su. Andai yi garkuwa da mutanen ne a makon da ya gabata, a kan hanyar su ta komawaLafiya daga Keffi. KakakinRundunar ’Yan Sanda ta jihar Nasarawa Sama’ila Juma’a a Lafiya cewa masugarkuwar sun sako matan da misalign karfe 9:45 na daren Alhamis da ta gabata. Yace masu garkuwar sun saki matan ne saboda matsin lambar bincike da neman su dajami’an tsaro su ka rika yi. Yace dukkan matar da aka kamac din, sun je yin rajistar aikin bautar kasa ne asansanin NYSC da ke Keffi, Jihar Nasarawa. Yace tuni kowace ta koma gida cikin iyalan ta. Sai dai Shugaban Kungiyar ’Yan Jaridar ya shaida wa manema labarai cewa, sai da ya biya kudi kafin a saki matar sa.
Politics Review
An Sako Matar Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida Da Sauran Matan Da Aka Kama A Jihar Nasarawa
Tags