Cacarbaki ta barke tsakanin jam’iyyun PDP da APC, bayan APC ta ba ‘ya’yanta umarninmamaye dukkan mukaman majalisar dokoki na kasa saboda su ke da rinjaye. Saidai jam’iyyar PDP ta kalubanci umarnin, inda ta bukaci ‘ya’yanta su yi takararkowane mukami da ke majalisar. Ashekara ta 2015 dai, jam’iyyar PDP ta shammaci jam’iyyar APC, inda Sanata IkeEkweremadu ya samu kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa, yayin da mukamanshugabannin majalisun biyu su ka shiga hannayen da jam’iyyar ta ce ba su kwantamata ba. Jam’iyyarPDP, ta ce babu wata doka da ta hana ‘ya’yan ta su nemi shugabancin majalisun tarayyada sauran muhimman kwamitoci. Sakaterenjam’iyyar PDP Sanata Ummaru Tsauri, ya ce tsarin mulkin Nijeriya bai ce dolesai wane ko wane ba za su shugabanci majalisun ba.
Suburbs Report
Takaddama: Jam’iyyun PDP Da APC Sun Sa Zare A Kan Shugabancin Majalisun Tarayya
Tags