Dakarun Syria da Amurkasun ce daular ISIS mai shekaru biyar ta zo karshe, bayan da aka dakushemayakanta a kasar Syria. Mayakan sun yi ta dagatutoci a Baghuz, gari na karshe da masu ikirarin jihadin ke rike da iko, a lokacinda take kan ganiyarta, kungiyar IS na da iko a kan fadin kilomita 88,000 afadin Syria da Iraki. Sai dai duk da kwaceiko daga kungiyar, ana tunanin tana ci gaba da zama babbar barazana ga tsaronduniya. Shugaba Trump ya yajinkirta janye dakarun Amurka daga Syria Har yanzu IS na nan ayankin kuma tana da rassa a kasashe da dama kamar Najeriya da Yemen da Afghanistanda kuma Philippines. Rundunar hadin gwiwa daKurdawa ke jagoranta ta fara yakinta na karshe da kungiyar IS ne a farkon watanMaris, inda sauran mayakan suka boye a kauyen Baghuz a gabashin Syria. An tilasta wa hadingwiwar rage bude wuta bayan da aka gano cewa akwai dimbin fararen hula a garin,zaune a gidaje, rumfuna da wasu maboya a karkashin kasa.
Water Digest
Syria : Har Yanzu Kungiyar ISIS Na Ci Gaba Da Zama Barazana
Tags