Jagoranjam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari kashedi a kantafarkin da ya kamata ya bi na tsare-tsaren gwamnatin sa a wa’adi na biyu. Tinubuya shawarci shugaba Buhari ya jajirce wajen dabbaka tsare-tsaren inganta jindadin jama’a domin ciyar da Nijeriya gaba kamar yadda ya yi alkawari yayinyakin neman zaben sa karo na biyu. BolaTinubu ya bayyana haka ne, a wajen bikin murnar cikar sa shekaru 67 a duniya,wanda ya gudana a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja, inda ya yi gargadincewa duk wani yunkuri da gwamnati ke yi ya kasance ya na da manufar fidda Nijeriyazuwa tudun mun tsira. Hakakuma, Tinubu ya yi kashedin cewa, yunkurin gwamnati na kara kudin haraji ba zaihaifar da komai ba face radadin talauci akan al’umma.